in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Kamaru ta tura tawaga domin sulhunta rikici tsakanin sojojin kasar
2015-05-29 10:03:05 cri

Bisa wani yunkurin sulhunta rikicin da ya barke a cikin rundunar sojojin kasar dake fagen daga domin yaki da kungiyar Boko Haram ta Najeriya, shugaban kasar Kamaru Paul Biya ya tura darekatan hulda da jama'a a fadar shugaban kasa, mista Martin Belinga Eboutou a yankin arewa mai nisa na kasar, a cewar wasu majiyoyin tsaro.

Darektan hulda da jama'a a fadar shugaban kasa ya isa wannan yanki a ranar Talata a karkashin wata tawagar dake kunshe shugabannin rundunar sojojin kasar, wadanda suka hada da babban hafsan hafsoshin sojojin kasar, janar Rene Claude Meka, a cewar wasu majiyoyi masu tushe da suka bukaci a boye sunayensu a wata hirarsu da kamfanin dillancin labarai na Xinhua. (Maman Ada)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China