Kotun kundin tsarin mulkin kasar Benin ta ba da umarnin dage zabukan kananan hukumomin birane da na lardunan kasar da wadanda aka shirya gudanarwa a baya a ranar 31 ga watan Mayu zuwa ranar 28 ga watan Yuni.
Bugu da kari, kotun ta gayyaci shugaban kasar ta Benin da ya sake hallara kan masu kada kuri'a don tattaunawa da kotun a ranar 26 ga watan Yuni.
Shugaban hukumar zaben kasar mai zaman kanta Emmanuel Tiando ya ce, sun bukaci a dage zabukan ne domin a gyara kura-kuran da aka gamu a lokacin zabukan 'yan majalisun dokokin kasar da aka yi a ranar 26 ga watan Afrilu.
Zabukan na ranar 28 ga watan Yuni, su za su ba da damar zaben kansiloli, magadan gari da mataimakansu wadanda za su kula da harkokin birane da kananan hukumomin kasar a wani wa'adi na uku bisa tsarin demokiradiya da kasar ta Benin ke ci gaba da aiwatarwa tun shekarar 1990.(Ibrahim)