Ma'aikatar harkokin cikin gidan kasar Afrika ta Kudu (DHA) ta sanar a ranar Talata cewa, dukkan yara dake shigowa ko fitarwa daga Afrika ta Kudu ya kamata su tanadi takardar haifuwa baya ga fasfonsu, tun daga ranar daya ga watan Yunin bana.
Ya kamata takardar haifuwa ta kasance tana kunshe da bayanan mahaifan yaron, in ji mista Mkuseli Apleni, darekta janar na DHA, a yayin wani taron manema labarai a birnin Cape Town. Mista Appleni ya kare wannan mataki mai tattare da cece-kuce, wanda tuni ya sanya wasu kasashe damar kafa wasu dokoki kan wannan batu.
Kasashe kamar Amurka, Burtaniya, Australiya da ma wasu kasashen Turai sun cimma irin wadannan bukatu, in ji mista Apleni.
A cikin wani hali inda mahaifi guda ke tafiya tare da yaro, matakin na bukatar ma'haifin ya kasance yana rike da wata takardar shaida dake cewa, mahaifin guda ya amince da yaron ya yi tafiya ba tare da shi ba.
Haka kuma, mista Apleni ya jaddada cewa, iyayen da ba su da aure, da kuma babu wasu bayanan da suka shafi mahaifin guda kan takardar haifuwa za su kaucewa wannan mataki.
Haka kuma mutanen dake bulaguro tare da yaron da ba nasu ba dole su gabatar da wata takardar shaida dake tabbatar da amincewar iyayen yaron.
Kimanin yara miliyan 2,7 suka yi bulaguro ta iyakokin kasar a shekarar 2014, wanda kuma kimanin miliyan 1,8 yara ne daga kasashen waje. Gwamnatin Afrika ta Kudu ta bayyana cewa, wadannan sabbin matakai za su taimaka wajen yaki da fataucin yara. (Maman Ada)