Shugaban kasar Afirka ta Kudu Jacob Zuma, ya ce, ya zama wajibi al'ummar Afirka su zamo tsintsiya madaurin kai daya, ta yadda za su cimma nasarar zama da juna lami lafiya.
Zuma wanda ya bayyana hakan a jiya Talata, lokacin da yake gabatarwa majalissar dokokin kasarsa kasafin kudin bana, ya kara da cewa, al'ummar Afirka ta Kudu na nunawa duniya kaunarsu ga zaman lafiya, tare da abuta mai dorewa tsakanin su da sauran al'ummun nahiyar Afirka.
Shugaban na Afirka ta Kudu dai ya dauki lokaci yana tsokaci game da tarzomar kin jinin baki da ta auku a watan da ya gabata, wadda ta yi sanadiyyar rasuwar mutane 7, kana daruruwan baki mazauna kasar suka tserewa gidajen su, baya ga shaguna da dama da aka wawashe.
Ya ce, gwamnatinsa ta umarci jami'an tsaro da su gudanar da bincike, tare da gurfanar da masu hannu cikin wannan lamari gaban kuliya. Hakan a cewar sa zai zamo darasi ga masu burin tada zaune tsaye. (Saminu)