Kasar Kamaru za ta zamanto mai masaukin baki na taron kungiyar tattalin arzikin kasashen Afrika ta tsakiya domin tattaunawa a kan yaki da 'yan kungiyar tsagera ta Boko Haram na Nigeria.
Shugabannin yankunan dabam-dabam na Afrika sun amince da gudanar da wannan taro a ranar 16 ga watan Fabarairun da muke ciki a lokacin taron kolin kungiyar hadin kan Afrika wanda aka yi kwanan nan a Habasha.
A yayin taron kolin kungiyar hadin kan kasashen Afrika, shugabannin sun duba barazanar kungiyar Boko Haram a kasasr Nigeria da kuma kasashe makwabta.
Taron ya jinjinawa shugaban Kamaru Paul Biya saboda yakin da yake yi da 'yan kungiyar ta Boko Haram a kasasrsa.
Hakazalika taron ya yabawa nasarorin da dakarun kasar Chadi suka samu a yakin da suke yi da 'ya'yan kungiyar tun bayan da aka tura su kasar Kamaru a tsakiyar watan Janairu.
Taron shugabannin kasashen AU ya kuma amince da samar da wasu kudurorin tsaro na yankin Afrika ta yamma domin marawa Kamaru da Chadi baya a kokarin da suke yi na yaki da kungiyar Boko Haram.
A watan da ya gabata ne kungiyar ta AU a karkashin kwamitinta na tsaro da zaman lafiya ta kirkiro da wata rundunar hadin gwiwa ta dakaru 7,500 domin yaki da kungiyar Boko Haram. (Suwaiba)