in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
An halaka mayakan Boko Haram a kalla 300 a Kamaru
2015-02-05 10:08:50 cri

Wata majiyar soja da ta bukaci a sakaye sunanta ta bayyana cewa, a kalla mayakan Boko Haram 300 ne aka halaka yayin wata musayar wuta da sojojin hadin gwiwar kasashen Kamaru da Chadi suka yi da mayakan na Boko Haram a yankin arewa mai nisa na kasar ta Kamaru.

Majiyar ta shaidawa kamfanin dillancin labarai na Xinhua na kasar Sin cewa, yayin fadan na ranar Labara da yamma, an kashe sojojin kasar Chadi 16 da na Kamaru 7 a yankin Fotokol dake kan iyaka da Najeriya baya ga fafaren hula da dama, ciki har da musulmai 30 da mayakan na Boko Haram suka halaka a lokacin da suke sallah a masallaci.

Bayanai na cewa, kimanin 'yan Boko Haram 7,000 ne suka yiwa garin na Fotokol dirar mikiya da safe, lamarin da ya tilastawa mazauna yankin barin gidajensu. Ko da yake jami'an tsaron hadin gwiwa sun sake kwato garin na Fotokol 'yan sa'o'i kadan bayan tashin hankalin.

A ranar 16 ga wannan wata ne shugabannin kasashen kungiyar ECCAS za su gudanar da wani taron koli a birnin Yaounde na kasar Kamaru don tattauna batun kafa rundunar hadin gwiwa mai kunshe da dakaru 7,500 da kungiyar AU ta yanke shawarar kafawa yayin taron kolinta na baya-bayan da ya gudana a birnin Addis Ababa na kasar Habasha don yakar kungiyar ta Boko Haram. (Ibrahim)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China