Rahotanni daga tarayyar Najeriya, na cewa, dakarun sojin kasar sun sake ceto karin mata da yara kanana su kusan 25 daga wasu sansanonin Boko Haram, bayan sun fatattaki mayakan kungiyar a ranar Laraba.
A cewar mai magana da yawun rundunar sojin Kanar Sani Usman, sojojin na ci gaba da kai hare-hare a sansanonin Boko Haram dake dajin Sambisa mai makwaftaka da jihar Borno a arewa maso gabashin kasar.
Usman ya kara da cewa, yayin farmakin da sojojin suka kaddamar, sun hallaka mayakan kungiyar da dama, tare da kwace makamai masu yawa. A daya hannun daya daga sojojin ya rasu, kana 5 sun samu raunuka.
A cewarsa, dakarun sojin na Najeriya ba za su yi kasa-a-gwiwa ba, wajen tabbatar da sun murkushe kungiyar Boko Haram baki daya. Ya ce, a wannan karo sojojin sun lalata sansanonin kungiyar 7, da kuma makamai masu yawa da mayakan ke amfani da su.
Farmakin da sojojin ke kaddamarwa daga makon jiya zuwa yanzu dai ya ba da damar ceto mata da yara sama da 500 daga dajin na Sambisa, dajin dake matsayin mafaka ta karshe ga mayakan na Boko Haram.
Kawo yanzu dai rahotanni na cewa, ba a kai ga ceto 'yan matan nan na Chibok su sama da 200, da Boko Haram ke tsare da su sama da shekara guda ba. (Saminu)