in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Bankin BRICS ba zai gasa da IMF, in ji shugabar Brazil
2014-07-17 09:31:19 cri

Shugabar kasar Brazil Dilma Rousseff a jiya Laraba ta ce, sabon bankin cigaba da kungiyar kasashen BRICS za ta kafa ba zai gasa da asusun ba da lamuni na duniya IMF.

Madam Rousseff, lokacin da take bayani ga manema labarai sakamakon ziyarar firaministan kasar India Narendra Modi, ta ce, ko da wasa ba su da ra'ayin yin gasa da asusun.

Brazil da India dai suna cikin mambobin kungiyar kasashe na BRICS da suka hada da kasar Sin, Rasha da kuma Afrika ta Kudu. A lokacin babban taronsu karo na shida a birnin Fortaleza na kasar Brazil din, kasashen biyar sun amince su kafa bankin cigaba, tare da ajiyan wani kaso na musamman kowanensu.

Sabon bankin cigaban NDB wanda zai yi aiki a madadin bankin duniya da asusun ba da lamuni na duniya, yana da matukar muhimmanci ga kasashen BRICS domin zai sauya yanayin tattalin arzikinsu, in ji shugaba Dilma Rousseff.

Sai dai a wani bangaren, wannan sabon bankin a ko da yaushe zai tsaya a matsayi na daban daga kasashen da IMF take hulda da su, amma, in ji madam Rousseff, a iya sanin asusun IMF, wannan bankin na da ra'ayin kara samun wakilta da aiwatar da demokradiya a tsarinsa. (Fatimah)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China