in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Shugaba Zuma ya bukaci 'yan kasar Afirka ta Kudu da su yi bikin ranar Afirka
2015-05-19 09:54:16 cri

Shugaba Jacob Zuma na Afirka ta Kudu ya bukaci 'yan kasarsa da su yi bikin ranar Afirka na wannan shekara wato ranar 25 ga watan Mayu ta hanyar nuna tarin al'adun da Allah ya hore wa kasar.

Zuma ya kara da cewa, wannan rana wata dama ce ta kara ilimantar da jama'a game da gudummawar da nahiyar Afirka ta ba da ga gwagwarmayar kasar Afirka ta Kudu ta neman 'yanci.

Shugaba Zuma ya ce, baya ga rawar da kungiyar hada kan kasashen Afirka wato OAU ta wancan lokaci ta taka wajen samun 'yancin kan kasar, su ma galibin kasashen nahiyar sun samar da mafaka ga 'yan kasar da dama da suke gudun hijira. Sannan sun samar da taimakon kayayyaki, goyon bayan siyasa da na soja, da kuma abubuwan jin dadin rayuwa da sauransu.

Don haka ya ce, wannan rana tamkar wata dama ce ta nuna cewa, nahiyar Afirka a hade take, kuma za a ci gaba da bayyana hakan ta hanyar goyon bayan da aka dade ana bayarwa a nahiyar da tashin hankali ya dabaibaye.

Shugaba Zuma na fatan ta hanyar wannan biki, kasar Afirka ta Kudu za ta nanata goyon bayanta ga ajendar AU na shekara 2063, tare da ganin kasar ta shiga cikin harkokin AU don ganin an samu nasarar aiwatar da manufofi da shirye-shryen da aka tsara na gina nahiyar Afirka mai wadata.(Ibrahim)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China