in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Shugaba Zuma ya jagoranci ranar Afirka
2015-05-25 10:37:31 cri

Shugaban kasar Afirka ta Kudu Jacob Zuma ya jaddada alkawarin ci gaba da hada kai da sauran kasashen Afirka, domin tabbatar da hadin kai da ci gaban nahiyar.

Zuma wanda ya bayyana hakan yayin bikin ranar Afirka wanda ya jagoranta a jiya Lahadi a Mamelodi dake birnin Pretoria, ya ce, wannan rana na da matukar ma'anar tarihi, kasancewarta lokaci da ake nazartar kalubalolin dake addabar nahiyar.

Shugaban na Afirka ta Kudu ya kara da cewa, a matsayin kasarsa na mai karbar baki daga sassan Afirka daban daban, Afirka ta Kudu za ta zama gida ga kowa, za kuma ta ci gaba da kasancewa jigon hadin kai ga al'ummar nahiyar cikin lumana da abota.

Kalaman na shugaba Zuma dai na nuni ga kudurinsa na tabbatarwa baki mazauna kasarsa cewa, za su samu kariyar da ta dace, bayan tarzomar kin jinin baki da ta auku a kwanakin baya.

An dai saba gudanar da wannan biki ne domin tunawa da kafuwar kungiyar hadin kan nahiyar ta OAU a shekarar 1963, kungiyar da daga bisani ta sauya zuwa AU a shekara ta 2002. Kaza lika bikin na ba da damar nazartar irin ci gaban da aka samu a fannin bunkasa dimokaradiyya, da zaman lafiya da daidaito, tare da bunkasar tattalin arzikin nahiyar. (Saminu)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China