in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
UNICEF na damuwa game da karancin ruwan sha a sansanin 'yan gudun hijirar Sudan ta Kudu
2014-04-23 10:26:08 cri

Wakilin asusun yara na MDD UNICEF dake Sudan ta Kudu Jonathan Veitch, ya bayyana damuwa game da karancin ruwan sha, da al'ummun dake samun mafaka a sansanin 'yan gudun hijirar Sudan ta Kudu ke fuskanta.

Hakan dai na kunshe ne cikin wata sanarwa da ofishin asusun na UNICEF ya fitar, wadda kuma ke cewa, halin da ake ciki ya tilasta baiwa ko wane mutum, abin da bai wuce lita guda na ruwan sha a kowace rana.

'Yan gudun hijirar wadanda suka tserewa tashin hankalin da ya auku a Bentiu cikin makon jiya, sun tsinci kan su cikin wannan mawuyacin hali ne, a daidai lokacin da kungiyar shuwagabannin kasashen gabashin Afirka ta IGAD, ta dage zagaye na biyu, na zaman tattaunawar da ake yi domin kawo karshen rikicin kasar da ya shafe watanni 4 yana gudana.

Sanarwar ta kara da cewa, asusun na UNICEF na kara ga daukacin sassan da rikicin kasar ya shafa, da su tabbatar da ba da kariya ga yara kanana, tare da tallafawa gudanar ayyukan jin kai. (Saminu)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China