in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
AU da MDD sun bukaci karin kokarin shawo kan cin zarafin jinsi a Somaliya
2015-03-04 10:34:48 cri

Manzannin MDD da kungiyar AU sun yi kira da a hada hannu wuri daya domin samar da matakan kare mata da 'yan mata a kasar Somaliya, kamar yadda mukaddashin kakakin MDD Vannina Maestracci ta sanar wa manema labarai.

Vannina Maestracci ta yi bayanin cewa, manzon musamman na MDD dake Somaliya, Nick Kay da kuma Maman S. Sidikou, manzon musamman na shugaban kwamitin kungiyar AU sun jaddada kudurinsu na goyon bayan kokorin kawo karshen cin zarafin da ya shafi mata da jinsi a Somaliya.

Madam Vannina ta yi bayanin cewa, manzannin biyu sun kuma jaddada muhimmancin samar da taimako da ya dace kamar kiwon lafiya da walwalar tunani ga wadanda suka fuskanci cin zarafi kowane iri har ma da iayalinsu.

MDD ta ba da rahoton cewa, an samu rahotanni 800 na cin zarafi da suka shafi mata da jinsi a Mogadishu, babban birnin kasar ta Somaliya kadai a cikin farkon watanni 6 a shekara ta 2013, duk da ana ganin adadin ya fi haka kwarai.

Gwamnatin Somaliya da MDD sun rattaba hannu a kan jawabin bayan taro a kan ba da kariya game da cin zarafin mata a watan Mayun shekarar 2013, tare da jaddada cewa, ba za'a lamunci saba wannan yarjejeniyar ba, kuma za'a hukumta duk wadanda aka kama da laifin aikata hakan. (Fatimah)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China