Gwamnatin jihar Borno da ke arewa maso gabashin Najeriya ta yabawa dakarun kasar bisa kokarinsu na kwato kimanin yara da mata 500 daga hannun mayakan Boko Haram a dajin nan nan Sambisa.
Cikin wata sanarwa da gwamnan jihar Borno Kashim Shettima ya rabawa manema labarai a garin Maiduguri, babban birnin jihar Borno, gwamnan jihar ya bayyana lamarin a matasyin abin farin ciki. Gwamna Shettima ya kuma kara da cewa, gwamnatinsa na dora muhimmanci kan kare rayuka, tsaro da kuma jin dadin rayuwar mazauna jihar.
Don haka ya bukaci dakarun kasar da su ci gaba da kokarin da suke yi wajen ganin sun kubuto sauran mutanen da ake tsare da su a dajin, ya kuma bayyana fatan cewa, sojojin kasar za su ceto 'yan matan sakandaren nan na garin Chibok cikin dan kankanin lokaci.
Idan ba a manta ba, a makon da ya gabata ma sojojin sun ceto wasu karin mata sakamakon harin da suka kaddamar a dajin na Sambisa.(Ibrahim)