Wani harin kunar bakin wake da ya abku a wata tashar motoci dake Potiskum, na jihar Yobe dake arewa masu gabashin Najeriya ya halaka mutane bakwai, tare da jikkata mutane 45. Wani 'dan kunar bakin wake ne ya tada bam a cikin wata motar a wannan tashar motocin, in ji Sulaiman Ahmed, wani wanda lamarin ya faru gaban idonsa. An gano gawawwaki hudu har da ta 'dan kunar bakin waken a wurin a yayin da mutane 48 sun jikkata.
Daga baya kuma, mutum guda ya mutu bisa hanyar zuwa asibiti, kana wasu mutane biyu sun mutu a yayin da suke samun jinya a asibiti, a cewar Sulaiman Ahmed. (Maman Ada)