in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Dakarun gwamnatin Sudan ta Kudu na rike da ikon garin Malakal
2015-05-26 09:44:48 cri

Mahukuntan kasar Sudan ta Kudu sun ce, sojojin gwamnati sun fatattaki mayaka masu biyayya ga tsohon shugaban kasar Riek Machar daga birnin Malakal, fadar jihar Upper Nile mai arzikin mai.

Hakan, a cewar ministan watsa labarun kasar Michael Makuei, ya biyo bayan kazamin fadan da sassan biyu suka gwaza a ranar Litinin. Makuei ya kara da cewa, sojojin gwamnatin sun samu nasarar amshe dukkanin muhimman wurare da 'yan tawayen suka yi yunkurin karbewa.

Tashe-tashen hankula dai na tsananta a jihohin Unity da Upper Nile, musamman ma a baya bayan nan, lamarin da ya sanya kungiyar hadin kan Afirka ta AU, bayyana bukatar kakabawa kusoshin 'yan adawar kasar takunkumi.

A daya hannun kuma, kwamitin tsaron MDD ya yi Allah wadai da kazantar halin da ake ciki a kasar, yana mai barazanar sanyawa masu aniyar dagula al'amura a kasar takunkumi. Sai dai tuni shugaban kasar Salva Kiir Mayardit ya bayyana hakan, a matsayin matakin da ba zai warware matsalar kasar ba.

Sudan ta Kudu wadda ta samu 'yancin kai a shekarar 2011, ta tsunduma cikin tashe-tashen hankula ne a watan Disambar 2013, lamarin da ya haddasa kisan dubban 'yan kasar, yayin da kuma wasu kusan miliyan biyu suka tserewa gidajensu. (Saminu)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China