in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
IGAD ta bukaci shugaba Al-Bashir da shiga tsakani a rikicin Sudan ta Kudu
2015-05-25 11:08:56 cri

Rahotanni daga kasar Sudan na cewa, kungiyar raya gabashin Afirka ta IGAD, ta bukaci shugaba Omar al-Bashir da ya shiga tsakani a rikicin kasar Sudan ta Kudu, duba da yadda har yanzu tashe-tashen hankula ke ci gaba da addabar makwafciyar kasar tasa.

Rikici dai na kara tsananta a Sudan ta Kudu, musamman ma a baya-bayan nan, inda tsagin sojojin gwamnati da dakarun 'yan adawar kasar ke dauki ba dadi da juna a jihohin Unity da Upper Nile masu arzikin mai.

Bisa wannan dalili ne kuma, kungiyar hadin kan Afirka ta AU, ta furta bukatar kakabawa bangaren 'yan adawar kasa takunkumi, tare da hana samar musu da makamai.

Kaza lika cikin makon da ya gabata, kwamitin tsaron MDD ya yi Allah wadai da barkewar sabbin tashe-tashen hankula a kudancin kasar, yana mai bayyana niyar makalawa takunkumi, ga dukkanin wadanda aka samu da laifin tada zaune tsaye a Sudan ta Kudun.

Amma shugaban Sudan ta Kudun Salva Kiir Mayardit, ya yi kashedin cewa, sanyawa kasarsa takunkumi, ba zai haifar da komai ba, sai dada dagula al'amura. (Saminu)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China