in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Sama da baki 'yan kasashen waje 5600 ne suka koma kasashensu daga Afirka ta Kudu
2015-05-18 09:50:58 cri

Mahukuntan Afirka ta Kudu sun bayyana cewa, sama da baki 'yan kasashen waje 5,645 ne aka tusa keyarsu zuwa kasashensu daga kasar tun lokacin da aka kawo karshen hare-haren kin jinin bakin da ya faru a kasar a karshen watan Afrilu.

Minista a fadar shugaban kasar Afirka Jeff Radebe wanda ya tabbatar da hakan ga manema labarai ya ce, galibin wadanda suka bar kasar 'yan kasashen Malawi, Mozambique da kuma Tanzaniya ne.

Radebe ya kara da cewa, sashen kula da jin dadin jama'a na kasar na ci gaba da aiki kafada da kafada da sauran sassan da kungiyoyin fararen hula don taimakawa bakin da wannan hare-hare ya shafa.

Ministan ya kuma kare manufar samamen da gwamnatin kasar ke yi kan bakin hauren da ke zaune a kasar ba bisa ka'ida ba, matakin da ministan ya ce, ana yi ne da nufin magance matsalar tsaro, tare da daidaita al'amura kamar yadda doka ta tanada.

Kasar Afirka ta Kudu ta fara daukar matakin tusa keyar bakin haure da ke zaune a kasar ne, bayan da aka kawo karshen boren kin jinin bakin da ya barke a kasar a watan da ya gabata. (Ibrahim)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China