in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
An bude taron tattaunawa game da rikicin siyasar Burundi
2015-05-22 10:21:47 cri

A jiya Alhamis ne aka bude wani zama na tattaunawa, tsakanin masu ruwa da tsaki game da dambarwar siyasar kasar Burundi, zaman da ke samun goyon bayan Said Djinnit, wakilin musamman na babban magatakardar MDD a yankin manyan tafkunan Afirka.

Mahalarta wannan zama dai sun hada da wakilan gwamnatin kasar, da wakilan 'yan adawa, da malaman addinai. Ana kuma sa ran tattaunawar da za a gudanar, za ta share fagen gudanar sahihin zabe, cikin kwanciyar hankali da lumana a kasar ta Burundi.

Da yake karin haske game da taron, kakakin MDD Farhan Haq, ya ce, daukacin sassan mahalarta taron na da rawar takawa, wajen warware halin da ake ciki, da samar da kyakkyawan yanayin wanzar da zaman lafiya, ta yadda za a kai ga gudanar da babban zabe wanda kowa zai amince da shi.

Haq ya kara da cewa, tarzomar da ta barke a kasar Burundi, ta tilastawa al'ummar kasar 110,000 kauracewa gidajensu zuwa makwaftan kasashe.

A wani ci gaban kuma, rahotanni na cewa, cutar kwalara ta barke a wasu sansanonin 'yan gudun hijirar dake kasar ta Burundi, wadanda ke makwaftaka da tafkin Tanganyika. Tuni kuma asusun yara na MDD ya fara aikin jin kai a wuraren da wannan cuta ta bulla. An ce, ya zuwa yanzu cutar ta kwalara ta riga ta hallaka mutane 27. (Saminu)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China