Ministan harkokin wajen kasar Burundi ya sanar a ranar Litinin cewa, MDD ta dauki niyyar cigaba da ba da tallafin kudi ga sojojin kasar Burundi dake cikin tawagogin wanzar da zaman lafiya na MDD, duk da cewa kasar ta kori wani mashawarcin MDD.
Muna fatan MDD za ta cigaba da kulawa ga dakarun kasar Burundi dake cikin ayyukan wanzar da zaman lafiya da suke a kasar Somaliya, Afrika ta Tsakiya, ko kuma wani wuri, domin wadannan sojoji na samun yabo daga wajen abokan kasashe dake tura rukunonin sojojinsu cikin irin wadannan ayyuka, in ji kakakin ma'aikatar harkokin wajen kasar Burundi, mista Daniel Kabuto a ranar Litinin a cikin wata hira ta kafar rediyo da talabijin ta kasar Burundi. (Maman Ada)