Manzon musamman na magatakardar MDD, Cassam Uteem ya yi kiran da a samar da damar zaman tattaunawa da amincewar juna tsakanin dukkan jiga jigan siyasar kasar Burundi kafin babban zaben dake tafe a watan Mayu.
Cassam Uteem wanda kuma shi ne shugaban tawagar sa ido kan babban zaben na Burundi ya ce, halin da ake ciki a kasar na bukatar yawan tattaunawa da tuntubar juna tsakanin hukumomi da sauran jam'iyyun siyasa bayan da ya gana da shugabannin jam'iyyun kasar, kungiyar matasa, kungiyoyi masu zaman kansu da kuma kafofin watsa labarai.
Shugaban tawagar sa ido a kan zaben ya bukaci da a sa ido kwarai a kan ayyukan zaben kasar da aka fara gudanarwa tun daga ranar 12 ga watan Janairu. Kuma tawagarsa za ta sa ido a kan zabuka biyar da za'a yi tsakanin watannin Mayu zuwa Satumba da suka hada da na shugaban kasar a ranar 26 ga watan Yuni.
Pierre-Claver Ndayicariye, shugaban hukumar zaben kasar ta Burundi mai zaman kanta tun da farko ya ce, daya daga cikin kalubalen da zaben ke fuskanta shi ne zuzuta labarai da kafofin yada labarai ke yi, da zaman dar dar dake tsakanin bangarorin matasa na jam'iyyun daban daban wanda wani abu ne ke dakusar da shirin gudanar da zaben. (Fatimah)