Ma'aikatar harkokin kasashen wajen kasar Faransa ta ce, tana kyautata zaton cewar, wani 'dan kasarta ya rasa ransa, bayan wata kungiyar hadin kai ta Jihadi ta yammacin Afrika a kasar Mali, wacce ke da alaka da al-Qaeda MUJWA ta yi awon gaba da shi shekaru biyu da suka wuce.
Kakakin ma'aikatar harkokin wajen Faransa Romain Nadal, ya ce, wata sanarwa daga kungiyar MUJWA, wacce ake zargi da sace mutumin, ya sanya a yanzu, suna kyautata zaton cewar, Rodriguez-Leal ya mutu, duk kuwa da yake cewar, babu wata shaida a zayyane da za ta bayar da tabbacin mutuwarsa.
Tun farko dai ita kungiyar MUJWA ta shaidawa kamfanin dillancin labaru na Faransa Agence France Presse cewar, an kashe wanda ake garkuwa da shi saboda Faransa makiyarsu ce.
Shi dai wanda aka sacen, watau Leal, 'dan sheakar 63 a duniya, duk da kasancewarsa 'dan kasar Faransa, an haife shi ne a Portugal ya kutsa kasar Mali daga Mauritania a cikin mota a watan Nawumbar shekarar 2012, a inda kwatsam sai aka yi awon gaba da shi a tsakanin kan iyakar kasashen Mauritania da Senegal.
A wata sanarwa ta dabam, shugaban Faransa Francois Hollande ya yi alkawarin daukar duk matakin da ya dace, domin gano abin da ya faru da Mr. Leal. Ya kuma ce, za'a hukunta duk wanda aka samu da laifin yin awon gaba da Mr. Leal. (Suwaiba)