A ranar Laraba 13 ga watan nan ne fadar shugaban kasar Faransa ta Elysee, ta fidda wata sanarwa dake cewa, shugaba Fracios Hollande ya zanta da shugaban Nigeria Goodluck Ebele Jonathan ta wayar tarho, inda shugabannin biyu suka yi musayar ra'ayi don gane da rikicin kasar Mali.
Shugabannin biyu dai sun yi ittifaki kan dacewar ayyukan soji da hadakar rundunonin Faransa, da na Afirka ke yi, domin fatattakar 'yan tawaye daga arewacin kasar ta Mali, tare da taimakawa mahukuntan kasar kwato yankunanta daga dakarun na 'yan tawaye.
Bugu da kari, sun tattauna kan yunkurin da aka yi na ceto 'yan Faransan nan, da wasu 'yan bindiga suka yi garkuwa da su a Nigeria. Daga nan sai shugaba Hollande ya godewa mahukuntan Nigeria, bisa kokarin da suka yi don gane da hakan. Makwanni 3 dai ke nan da aka sace mutanen 7 'yan asalin kasar ta Faransa daga jamhuriyar Kamaru, aka kuma tisa keyarsu zuwa Nigeria, kuma wadanda suka yi garkuwar da su suka yi barazanar kashe su, muddin ba a saki 'yan uwansu dake hannun mahukuntan Nigeriar ba.
Garkuwa da mutanen dai ta zo daidai lokacin da sojojin sa kai na hadin gwiwar Faransa da Afirka, ke ci gaba da yaki da 'yan tada kayar baya a arewacin Mali, da nufin taimakawa mahukuntan kasar wajen fatattakar su.(Saminu)