in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Hankula sun fara kwanciya a Afirka ta Kudu bayan tashe-tashen nuna kyamar baki
2015-04-20 10:21:23 cri

Rahotanni daga kasar Afirka ta Kudu na cewa ya zuwa ranar Lahadi, hankula sun fara kwanciya bayan tashe-tashen hankula da suka biyo bayan kyamar baki a sassan kasar daban daban.

An ce, yanzu haka babu sauran rahotanni na tashin hankali, ko fasa shaguna a biranen Durban da Johannesburg. Yayin da kuma 'yan sanda ke ci gaba da sanya ido game da yiwuwar sake barkewar tarzoma.

Tuni dai ministan ma'aikatar cikin gidan kasar Malusi Gigaba ya ba da tabbacin kawo karshen hare-haren da ake kaiwa kan baki mazauna kasar.

A daya hannun kuma shugaba Jacob Zuma da Mr. Gigaba, sun ziyarci wani sansani da aka tsugunnar da wadanda tashe-tashen hankulan suka raba da gidajensu su kusan 1,000, a yankin Chatsworth dake birnin Durban.

Yayin ziyarar tasu, shugaba Zuma ya ce, kasarsa za ta taimakawa wadanda ke fatan komawa kasashensu yadda ya kamata. Shi kuwa Gigaba cewa ya yi, ko shakka babu, jami'an tsaro za su tabbatar da ganin ba a sake kaddamar da hare-hare kan baki a dukkanin sassan kasar ba.

Duk dai da wannan alkawari na mahukuntan Afirka ta Kudu, wasu daga kasashen Afirka sun fara kwashe 'yan kasashensu zuwa gida, yayin da wasu kuma da dama ke ci gaba da shirin aiwatar da hakan. (Saminu)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China