in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
An rufe ofishin jakadancin Afirka ta Kudu dake Najeriya
2015-04-23 09:31:01 cri

Mahukunta a Najeriya sun ba da umarnin rufe ofishin jakadancin Afirka ta Kudu dake birnin Ikkon jihar Legas, domin kaucewa fushin masu zanga-zanga, dake nuna bacin ransu game da kyamar baki a Afirka ta Kudun.

A cewar jakadan Afirka ta Kudu dake Najeriya Sam Monaisa, rufe ofishin ya dace da bukatar kare rayukan ma'aikatansa. Ya kuma bukaci 'yan Afirka ta Kudu dake Najeriya da su yi taka-tsantsan, domin kaucewa hare-haren ramuwar-gayya daga masu zanga-zanga.

Cikin 'yan kwanakin nan dai 'yan Najeriya da dama na gudanar da jerin gwano a ofisoshin jakadancin Afirka ta Kudu, musamman a biranen Ikko da kuma Abuja, fadar gwamnatin kasar, inda wasu ke barazanar aukawa kadarorin kasar Afirka ta Kudun, a matsayin martani na kyama da ake nunawa baki 'yan kasashen waje a kasar.

Rahotanni sun nuna cewa, wasu daga masu boren sun baiwa Afirka ta Kudu kwanaki 3, da ko dai ta dauki matakin dakile hare-hare kan baki, ko kuma su farwa 'ya'yanta dake zaune a Najeriya.

Ya zuwa ranar Lahadin karshen makon jiya dai, hankula sun dan kwanta a biranen Durban da Johannesburg, inda rahotanni ke cewa ba a samu karin hare-hare ko fasa shaguna ba. Akwai dai 'yan Najeriya sama da 450,000 dake zaune a Afirka ta Kudu, wadanda a yanzu haka mafiya yawansu ke samun mafaka, a ofishin kula da harkokin cikin gidan Afirka ta Kudun dake birnin Pretoria. (Saminu)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China