Babban magatakardar MDD Ban Ki-moon, ya bayyana gamsuwa game da matakin da majalissar dokokin kasar Somaliya ta dauka, na amincewa da Omar Abdirashid Ali Sharmarke, a matsayin sabon firaministan kasar.
Cikin wata sanarwa da kakakinsa ya fitar game da wannan batu, Mr. Ban ya bukaci sabon firaminsiatan, da shugaban kasar, da ma shugaban majalissar dokokin kasar ta Somaliya, da su hada karfi da karfe wajen gudanar da ayyuka tare, domin tabbatar da dorewar tsarin gwamnatin tarayya a kasar.
Mr. Ban ya kuma yi kira ga daukacin masu ruwa da tsaki a siyasar kasar da su dauki dukkanin matakan da suka wajaba, don kaucewa sake aukuwar matsalolin siyasar da kasar ta fuskanta a baya.
A jiya Laraba ne dai aka ayyana sunan Omar Abdirashid Ali Sharmarke, a matsayin sabon firaministan kasar Somaliya, tuni kuma ya alkawarta kafa sabuwar gwamnati da za ta kunshi dukkanin sassan kasar.
Kafin nadin Sharmarke, shi ne manzon kasar ta Somaliya a Amurka, zai kuma maye gurbin Abdiwali Sheikh Ahmed, wanda majalissar dokokin kasar ta jefawa kuri'ar yanke kauna, bayan takun-sakar da ya ki ci ya ki cinyewa tsakanin sa da shugaban kasar Hassan Sheikh Mohamud. (Saminu)