in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Gwamnatin Benin ta fitar da jadawalin zabe bisa matsin lambar 'yan adawa
2014-12-15 11:02:41 cri

Gwamnatin kasar Benin ta gabatar wa jam'iyyun adawa ra'ayinta kan jadawalin zabe, inda an ce, za'a gudanar da zabukan kananan hukumomi a ranar 24 ga watan Maris din shekarar 2015, kana kuma zaben 'yan majalisar dokoki a ranar 26 ga watan Afrilun shekarar 2015, in ji sakatare janar na gwamnatin kasar Allasani Tigri a ranar Asabar.

Da yake gabatar da sakamakon taron ministoci a gidan talabijin na kasar, Allasani Tigri ya jaddada cewa, wannan jadawali na la'akari da ra'ayoyin hukumar zabe mai zaman kanta ta kasa da kuma hangen kwamitin tsare tsare da kula da rajistan zabe mai zaman kansa. (Maman Ada)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China