in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Kwace Ramadi da IS ta yi wani babban koma baya ne, in ji Amurka
2015-05-19 10:09:30 cri

Kasar Amurka ta lashi takwabin taimakawa dakarun tsaron Iraki na ganin an sake kwato garin Ramadi, hedkwatar lardin Anbar daga hannun mayakan IS.

Kakakin fadar White House ta Amurka Eric Schultz ya shaidawa maname labarai a kan hanyarsa ta zuwa Camden da ke New Jersey ta jirgin saman yakin Amurka cewa, mayakan IS sun kwace garin Ramadi, kuma wannan wani koma baya ne.

Ya ce, jiragen yakin Amurka za su ci gaba da yin luguden wuta kan sansanonin mayakan IS har sai an sake kwato garin na Ramadi. Ya kuma bayyan cewa, kawancen kasashen da Amurka ke jagoranta sun kaddamar da hare-hare ta sama har sau 32 kan cibiyoyin mayakan na IS cikin makonni uku da suka gabata don taimakawa kokarin da sojojin Iraki ke yi na kare garin Ramadi.

A ranar Lahadi ne mayakan na IS suka kwace garin Ramadi, bayan da sojojin Iraki suka janye daga inda suka ja daga.(Ibrahim)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China