in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Reshen kungiyar IS dake Libiya ya sanar da kisan wasu Kiristocin Habasha 30
2015-04-20 10:09:10 cri

A jiya Lahadi ne reshen kungiyar IS dake kasar Libiya, ya yi ikirarin kashe wasu Kiristoci 'yan kasar Habasha su 30. Reshen kungiyar ta IS ya kuma wallafa wani faifan bidiyo mai dauke da shirin harbe wadannan Kiristoci, tare da kuma yanke kawunansu a kan shafinsa na internet.

Faifan dai ya nuna yadda aka hallaka wasu mutane su 15 a bakin teku, kana aka harbe sauran mutanen su 15 a cikin wani daji.

Sai dai bayan fidda faifan, kasar Habasha ta ce ba a kai ga tabbatar da gaskiyar asalin mutanen da aka kashe ba tukuna, amma duk da hakan ta yi Allah wadai da aukuwar wannan ta'asa.

Rahotanni na cewa sakamakon tashe-tashen hanulanda ake ci gaba da fuskantawa a kasar Libiya, kungiyar IS ta samu zarafin habaka karfinta a kasar. Inda a tsakiyar watan Faburairun wannan shekara, reshen kungiyar dake Libiya ya hallaka wasu kibdawa 'yan kasar Masar su 21 ta irin wannan hanya.

Ban da haka kuma, a watan Janairun bana, reshen IS din ya bayyana daukar alhakin kisan wasu 'yan kasar Tunisiya su biyu. (Lami)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China