in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Amurka ba za ta ware zunzurutun kudade ba domin yakar kungiyar IS
2014-12-30 10:27:56 cri

Shugaban kasar Amurka Barack Obama ya ce, duk da kasancewar barazanar kungiyar Islama ta IS, wannan ba zai sa Amurka ta ware wasu makudan kudaden agaji ba domin yakar kungiyar mai tsattsauran ra'ayi.

A yayin da yake magana da rediyon kasar Amurka NPR, Obama ya ce, ko shakka babu kungiyar Islama tana da hadarin sosai, musamman idan aka yi la'kari da muradunta na mallake kasashe, da mallakar dakarun soji da albarkatun kasa.

Obama ya ce, kungiyar Islamar tana yin barazanar gaske ga kasashen dake kawance da Amurka a da, kuma illahirin yankin Gabas ta Tsakiya gaba daya.

A halin da ake ciki kungiyar IS ta tashi gadan-gadan wajen kwatar wuraren jama'a, kuma a yanzu haka ta kwace kashi daya bisa uku na yankunan kasashen Syria da Iraq.

Washington ita ce ke jagorantar kasashen yankin wajen kaiwa kungiyar farmaki daga sama a kasashen Syria da Iraqi, a kokarin da suke yi na murkushe kungiyar Islamar, to sai dai Obama ya ce, wargaza kungiyar zai dauki tsawon lokaci. (Suwaiba)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China