in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Afrika ta Kudu ta kame bakin haure
2015-05-11 14:52:52 cri

Kasar Afrika ta Kudu ta ce, ta kame bakin haure da dama lokacin wani aikin hadin gwiwwa, za'a mai da su kasashensu na asali. Kamar yadda wani jami'in gwamnatin kasar ya tabbatar a ranar Lahadin nan, an ce, babban kalubale ne ga kasar da ta mai da bakin haure masu yawan gaske da ta kame ya zuwa yanzu, amma ya ce, sashin kula da wannan aiki zai tabbatar da an mai da mutanen kasashensu na asali cikin kwanaki 30.

Gwamnatin kasar Afrikan ta Kudu tana ta duba takardun 'yan kasashen waje dake zaune a kasarta, galibinsu daga sauran kasashen Afrika sakamakon rikicin nuna kyamar baki da ya faru a kwanakin baya a wassu sassan kasar.

Yan sanda da sojoji na kasar sun kaddamar da wani aikin hadin gwiwwa da aka yi wa lakabin Fiela wanda a harshen Sotho ke nufin shara, kuma a ranar Asabar da ta wuce suka fara da wadanda ake zarge suna zaune ba da izini ba a birnin Durban da Johannesburg wadanda suke fi cunkoson jama'a, inda aka kame mutane fiye da 500. Ya zuwa yanzu dai akwai sama da mutane 1000 da suka shiga kasar ba da izini ba kuma ana rike da su da shirin mai da su kasashensu.

Sai dai wassu kungiyoyi masu zaman kansu a ranar Lahadin nan suna ganin wannan aiki ba'a yi shi a lokacin da ya dace ba, maimakon haka ma akwai alamun siyasa da a tattare da shi, abin da yasa wassu kungiyoyin suka yi zanga zanga a ofishin 'yan sanda dake Johannesburg domin nuna rashin jin dadin yadda ake farma wuraren da 'yan kasashen wajen ke zama. (Fatimah)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China