Shugaban rundunar sojojin tsaro na kasar Uganda Janar Edward Katumba Wamala ya ce, kasar Uganda ba za ta tura sojojinta zuwa Nigeriya ba domin yaki da kungiyar Boko Haram.
Janar Wamala ya shaidawa kaamfanin dillancin labarai na Xinhua ta wayar tarho cewar, kasar ta Uganda ba ta da wani shiri na tura sojojinta arewacin Nigeria a matsayin wani kokari na yanki domin dakile matsalar Boko Haram.
Tun farko wasu kafofin yada labara na kasar Uganda sun bayyana cewar, Ugandar za ta tura bataliyar soji guda 2 zuwa Nigeria a matsayin wani hobbasa na nahiyar Afrika domin murkushe rikicin da kungiyar Boko Haram ta haddasa a Nigeria.
Su dai dakarun na Uganda sun kasance suna gudanar da ayyukan kiyaye zaman lafiya a kasashen Somalia, Sudan ta Kudu, jamhuriyar Afrika ta Tsakiya inda suke yakar 'yan tsagera mafi kaurin suna na Lord's Resistance Army.
A makon da ya shude ne a yayin taron koli na kungiyar hadin kan Afrika AU a Addis Ababa, babban birnin Habasha, shugabannin kasashen Afrika suka amince da tura dakaru dubu 7,500 zuwa Nigeria domin tunkarar barazanar Boko Haram, tare da murkushe kungiyar.
Shugabannin na Afrika sun dauki matakin aikewa da sojoji Nigeriya a sakamakon rokon da kwamitin tsaro, da samar da zaman lafiya na kungiyar ta AU ya yi na neman amincewar AU game da tura dakaru daga kasashe biyar na Afrika ta yamma zuwa Nigeriya domin yakar kungiyar Boko Haram. (Suwaiba)