Kasar Uganda ta nuna yabo kan matakin da kasar Sin ta dauka na tura tawagogin sojojin wanzar da zaman lafiya a kasar Sudan ta Kudu, da kuma nuna goyon bayanta kan kokarin shiga tsakani na kungiyar IGAD domin kawo karshen yake yake a cikin wannan kasa.
Asuman Kiyingi, ministan harkokin wajen kasar Uganda, ya shaida wa manema labarai a ranar Talata a birnin Kampala cewa, kasar Sin za ta dauki muhimmin matsayi a cikin shawarwarin bangarorin dake yaki da juna a Sudan ta Kudu, wato shugaba Salva Kiir da tsohon mataimakinsa Riek Machar da yanzu shi ne shugaban masu adawa. (Maman Ada)