in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Rikicin kyamar baki ya haifar da koma baya ga harkokin yawon shatakawa na Afirka ta Kudu
2015-05-06 10:05:26 cri

Harkokin yawon shakatawa na kasar Afirka ta Kudu na fuskantar barazanar koma baya, sakamakon rikicin nuna kyamar baki na baya-bayan nan da ya barke a kasar.

Ministan harkokin yawon shakatawa na kasar Derek Hanekom wanda ya bayyana hakan ya ce, irin gargadin da kasashe da dama suka rika yiwa 'yan kasashensu da su guji zuwa kasar Afirka ta Kudu, zai yi mummunan tasiri ga bangaren harkokin yawon shakatawar kasar.

Kasashe kamar su Amurka da Burtaniya da Australia sun gargadi 'yan kasashensu da kada su je kasar Afirka ta Kudu idan ba da wani dalili mai kwari ba.

Bangaren yawon shakatawa dai shi ne na uku da ke samarwa kasar Afirka ta Kudu kudaden shiga, kuma gwamnatin kasar na fatan sashen zai rika samar mata kudaden da suka kai dala miliyan 600 a ko wace shekara tare da samar da sabbin guraben ayyukan yi dubu 225 ya zuwa karshen shekaru 10.

Amma rikicin nuna kyamar baki na baya-bayan da ya barke a kasar ya dakushe hasken wannan bangare wanda tuni ya rage kudaden da take samu idan aka kwatanta da na watanni 8 na farkon shekarar 2014. (Ibrahim)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China