in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Yawan wadanda suka halaka a harin da aka kai gidan yarin Mogadishu ya kai 12
2014-09-01 10:23:28 cri

Fadar shugaban kasar Somalia ta bayyana cewa, mutane 12, ciki har da jami'an tsaro 3 da fararen hula 2 ne suka mutu a harin da aka kai gidan yarin Mogadishu a ranar Lahadi, harin da kungiyar Al-Shabaab ta yi ikararin kaiwa.

Fadar shugaban kasar Somalia ta bayyana cewa, mayakan na Al-Shabaab sun kai harin ne da nufin huce haushi kan kwace muhimman garin nan na Mulo Marer da aka yi daga hannun su.

Tawagar AMISON ta sha alwashin kwace garin Baraawe mai tashar jiragen ruwa daga hannun mayakan na Al-Shabaab, daya daga cikin muhimman wuraren da ake samun kudaden shiga da ya rage a hannunsu.

Mayakan na Al-Shabaab sun kai harin kunar bakin wake ne da wata mota sheke da bam kan gidan yarin da ke cike da matakan tsaro da nufin kubutar da 'yan uwansu da ake tsare da su a gidan yarin, amma mayakan AMISON da sojojin gwamnati suka mayar da martini. (Ibrahim)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China