A jiya ne mayakan Al-Shabaab suka kaddamar da wani hari a kan sansanin dakarun wanzar da zaman lafiya na kungiyar AU (AMISOM) da ke Mogadishu.
Kakakin mayakan na Al-Shabaab Abdulaziz Abu Musab ya tabbatar da kai harin kan dakarun na AMISOM. Shi ma kakakin na AMISON Kanar Ali Houmed ya tabbatar da abkuwar lamarin, amma ya ce, dakarunsu sun yi nasarar kashe a kalla 'yan ta'adda 10 tare da kama wasu guda 2.
A jawabinsa, kakakin gwamnatin Somaliya Ridwan Haji, ya yi allahwadai da hare-haren da mayakan na Al-Shabaab suka kai a sansanin na AMISON da ke birnin Mogadishu. Inda ya bukaci dakarun na AMISON da su ci gaba da kokarin da suke na goyon bayan gwamnatin da al'ummar Somaliya.
Hedkwatar dakarun ta AMISON dai tana cikin sansanin Halane ne, wani bangare na filin jiragen saman kasa da kasa na kasar ta Somaliya da ke Mogadishu da kuma wasu ofisoshin jakadancin kasashen yammacin duniya. (Ibrahim)