Rahotanni daga kasar Somaliya na cewa, dakarun Amurka sun hallaka wani jigo a kungiyar Al-Shabaab, bayan da suka yi luguden wuta kan jerin gwanon wasu motace masu dauke manyan kusoshin kungiyar.
Kwamishi mai kula da yankin Garbaharey Mohamed Ali, ya shaida wa majiyarmu cewa, harin da aka kaddamar ta sama, ya ritsa da manyan dakarun na Al-Shabaab su uku, ciki hadda wani babban kwamandanta mai suna Aden Garar, a kan hanyarsu ta zuwa yankin Gedo dake kan iyakar Somalia da kasar Kenya.
Harin dai na ranar Alhamis ya auku ne 'yan sa'o'i kadan, bayan harin da Al-Shabaab din ta kaddamar, kan wani ofishin gudanarwar wani yanki dake tsakiyar kasar, harin da ya sabbaba rasuwar mutane 10, tare da raunata wasu da dama.
Dakarun Amurka dai sun kaddamar da hare-hare da dama ta sama kan mayakan na Al-Shabaab, tare da hallaka da dama daga shugabanninta.
Kuma kawo yanzu gwamnatin Somaliya, da bangaren kungiyar ta Al-Shabaab ba su ce komai ba tukuna, game da harin da dakarun na Amurka suka kaddamar. (Saminu)