in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Gwamnatin Nigeria ta umurci kamfanonin wutar lantarki da su dinga amfani da kayayyakin kasar
2014-12-12 16:16:24 cri

Gwamnatin tarayyar Nigeria ta umurci dukanin kamfanonin dake rarraba wutar lantarki na kasar da su dinga sayen kayayyakin lantarkin da aka hada a cikin kasar ta Nigeriya, domin hakan ya yi daidai da manufofin da gwamnatin ta kafa, wadanda aka tsara domin tabbatar da habbakar masana'antu a Nigeriya.

Ministan masana'antu da saka jari na Nigeria Olusegun Aganga shi ne ya bayar da wannan umurni a yayin wani taron kwararru a Nigeria, wanda ma'aikatar masana'antu da cinikayya da saka jari ta Nigeriya ta shirya tare da hadin gwiwar hukumar daidaita ayyukan kamfanonin samar da wutar lantarki ta Nigeria.

A cikin jawabinsa, ministan masana'antu ya ce, ma'aikatarsa ta samu koke da yawa na jama'a dake zargin cewar, kamfanonin wutar lantarkin sun ki sayen mitocin da aka hada a Nigeria a inda a maimakon hakan suke shigo da mitoci da transfoma daga kasashen ketare.

Ministan ya ce, manufar taron shi ne ya tara kwararru masu fada a ji domin su duba wannan kalubale dake tunkarar bangaren masana'antu na Nigeriya tare da bayar da shawarwari da tsare-tsare wadanda za su taimaka a zayyana manufofi da dokoki da suka dace da ci gaban bangaren.

Ministan ya kara da cewar, ya kamata a dauki mataki a bisa amannar da 'yan Nigeriya suka yi na cewar, kayayyakin wutar lantarki na cikin gida ba su da aminci bayan a fili take cewar kayayyakin da aka yi a gida Nigeriya amincinsu ya zarce na kasashen ketare. (Suwaiba)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China