Tarayyar Najeriya da kamfanin wutar lantarki na kasar Sin 'Xian Electric Engineering Company Limited' sun rattaba hannu a ranar Talata kan wata kwangilar dalar Amurka miliyan 500 domin fadada layoyin isar da wutar lantarki a dukkan fadin wannan kasa mafi yawan mutane a nahiyar Afrika.
An sanya hannu kan yarjejeniyar a gaban idon ministan makamashin Najeriya Chinedu Nebo da kuma shugabannin kamfanin Xian wanda aka fi sani da kamfanin China XD, lamarin dake bayyana kokarin kara karfafa zuba jari a bangaren samar da wutar lantarki a wannan kasa dake yammacin Afrika. Haka kuma wannan yarjejeniya za ta fara aiki nan take, kuma za ta kai har tsawon lokacin shekaru biyu, inda a cikin wannan lokaci, za'a kammala yawancin wannan aiki, in ji mista Nebo.
Kamfanin Xian ya kasance a yanzu haka daya daga cikin manyan kamfanonin da suka fi kwarewa a wannan fanni a duniya, ministan Najeriya ya tabbatar da cewa, kasarsa za ta cigaba da rike hulda tare da wannan kamfani na kasar Sin, wanda kuma daga nashi bangare, zai cigaba da bunkasa da kuma samar da layoyin isar da wutar lantarki da tashoshin karbar cigaban aikin domin kyautata shawagin wutar lantarki a dukkan fadin wannan kasa mai arzikin man fetur. (Maman Ada)