Shugaban shirin hadin gwiwa na bunkasa nahiyar Afirka NEPAD karkashin kungiyar AU Mosad Elmissiry, ya ce, nan da shekara ta 2020, kasashen nahiyar Afirka za su hade manyan layukansu na samar da wutar lantarki, a wani mataki na inganta samar da makamashin tsakanin kasashen nahiyar.
Shugaban shirin na NEPAD, ya shaida wa majiyarmu cewa, hade layukan lantarkin yankunan nahiyar hudu, zai zamo kashin-bayan hadin gwiwar nahiyar a fannin makamashin na lantarki.
Elmissiry ya kara da cewa, makasudin daukar wannan mataki shi ne bude kasuwar makamashin, ta yadda kasashen dake da rarar wutar za su iya sayar da ita ga sauran kasashe masu bukata.
Ya ce, mai yiwuwa ne yankin arewa maso kudanci, ya zamo na farko a karkashin wannan tsari, inda ake fatan hade manyan layukan lantarkin kasashen Afirka ta Kudu da Masar.
Sai kuma aikin hada kasashen Kenya da Tanzania, da na Kenya da Habasha, da Afirka ta Kudu da Zimbabwe, da kuma Masar da kasar Sudan, aikin da shi ma ake fatan zai kammala ba tare da wani cikas ba.
Yanzu haka dai jimillar lantarkin da nahiyar ta Afirka ke samarwa ya kai Mega-Wat 120,000, kuma Afirka ta Kudu da Masar ne ke samar da kaso mafi tsoka na daukacin lantarkin a nahiyar. (Saminu)