Hukumar bayar da agajin gaggauwa a Najeriya (NEMA) ta aike da wata tawaga zuwa garin Yola, fadar mulkin jihar Adamawa da ke arewa maso gabashin kasar don karbo mata da 'yan matan nan 293 da dakarun kasar suka ceto daga sansanonin mayakan Boko Haram a dajin Sambisa.
Kakakin hukumar ta NEMA Sani Datti ne ya tabbatar da hakan ranar Lahadi cikin wata sanarwa da aka rabawa manema labarai ya kuma bayyana cewa, dakarun kasar sun shaidawa hukumar cewa, sojojin na yiwa mutanen da aka ceto rakiya zuwa garin na Yola.
Sani Datti ya ce, hukumar ta yi dukkan shirye-shiryen da suka wajaba na tsugunar da mutanen da aka ceton.(Ibrahim)