Rahotanni daga Nigeriya sun tabbatar da cewa, sojojin kasar sun ceto wassu mata kusan 300 daga dajin Sambisa a jihar Borno dake arewa maso gabashin kasar, sakamakon tsaurara ayyukan dakile 'yan kungiyar nan ta Boko Haram.
Kakakin Rundunar tsaron kasar manjo janar Chris Olukolade wanda ya tabbatar da hakan ya ce, ba zai iya tantace wadanda aka kubutar ba ko kuma asalinsu, sannan ba ya da tabbacin ko daga cikinsu akwai 'yan matan Chibok, sai bayan an gama musu bincike da samun cikakkun bayanai game da su.
Janar Olukolade ya tabbatar da cewa, babu shakka da tsakar ranar Talatan nan, an samu gaggarumar nasarar ceto 'yan mata 200 da kuma manyan mata 93 a sansanoni daban daban dake cikin dajin, kuma yanzu haka ana binciken su tare da samun bayanai game da asalinsu.
Kakakin rundunar tsaron ya kara da cewa. a kalla manyan sansanonin 'yan kungiyar ta Boko Haram 3 dake dajin, an lalata su a wani farmakin da aka shirya cikin tsanaki da suka hada da sansanin Tokumbere a cikin dajin na Sambisa.
Kusan yara 'yan mata 300 ne kungiyar ta Boko Haram ta sace a shekarar bara a makarantar 'yan mata dake garin Chibok wadanda a cikin su 'yan kalilan ne suke kubuta, amma akwai a kalla 219 da har yanzu babu labarinsu.
Wannan satar 'yan matan ta harzuka kasashen duniya, duk da kuma alkawurran da kasashen yammaci suka yi na gano su da kuma kokarin kasar Chadi na tabbatar da kubutar da su, har yanzu ba'a gano yaran ba. (Fatimah)