Hukumar kula da 'yan gudun hijira ta MDD a ranar Talatan nan ta bukaci mahukunta a jamhuriyar democradiya ra Kongo DRC da cibiyar samar da daidaito ta MDD da su inganta kokarinsu wajen hana tashin hankalin dake ruruwa, saboda akwai matukar damuwa game da masifar da za ta biyo baya a gundumar Katanga.
A cewar hukumar 'yan gudun hijiran, tashin hankalin a kudu maso gabashin kasar ta DRC ya tilasta wa mazauna kusan 400,000 tserewa daga gidajensu tun barkewar fada a karshen shekarar 2012, abin da ya kawo jimillar wadanda suka rasa gidajensu zuwa 600,000. A cikin watanni 3 da suka gabata kadai, fiye da mutane 71,000 suka rasa gidajensu.
Hukumar ta yi amannar cewar, domin kawo karshen tashin hankalin, akwai bukatar kara yawan mahukuntar kasar a wuraren da ke fuskantar tashin hankalin, sannan a duba hanyoyin da za'a warware rikicin tsakanin al'ummar Luba da Twa.
Haka kuma ya kamata a mutunta 'yancin kabilu marasa yawa da kuma 'yan asalin wurin, musamman kabilar Twa, a ba su kariya da amincewa. Sannan yana da muhimmanci a kawo karshen mulkin kama karya da ake yi ba tare da kula da dokoki ba. Haka kuma, in ji hukumar, ya kamata a hana yaduwar makamai babu gaira babu dalili ta hanyar shirya wadansu ayyuka da kowa zai mika makamin shi domin a taimaka wa tsaffin masu rike da makamai samun wani aikin yi a cikin al'umma.
Hukumar 'yan gudun hijiran ta MDD ta yi kira ga ofishin wanzar da zaman lafiya na MDD a DRC da ta karfafa kokarinta da ayyukan da take yi a arewacin Katanga domin samar da kariya ga mazauna wajen, sannan a hana keta hakkin bil adama da ke faruwa a yanzu.
Kusan mutane miliyan 2.6 ne suka rasa muhallansu a kasar baki daya. (Fatimah)