Yakin kin jinin wasu yankuna, ko mulkin danniya na "Fascist", ya koyar da duniya wani babban darasi, wanda bai kamata tarihi ya mance da shi ba.
Wakilin din din din na kasar Sin a MDD Liu Jieyi ne ya bayyana hakan, yayin wani zaman musamman da aka gudanar ranar Talata a zauren MDDr, domin tunawa da wadanda yakin duniya na biyu ya shafa.
Mr. Liu ya ce, ya dace a rika tuna sakamakon hakan a matsayin wata hanya ta nunawa duniya muhimmancin zaman lafiya, domin a cewarsa, tuna tasirin yake-yake, na iya sanya bil'adama fahimtar alfanun zaman lafiya.
Manzon na Sin ya kara da cewa, a bana ne ake cika shekaru 70 da cimma nasarar kawo karshen yakin amfani da karfin tuwo, da kuma kafuwar MDD, kuma kasar Sin ta gudanar da wasu ayyuka na tunawa da hakan, ciki hadda bikin tunawa da kin jinin harin Japanawa.
Mr. Liu ya ce, wannan biki na da matukar muhimmanci, kuma Sin na ci gaba da nuna alhinin rasa rayukan fararen hula da aka yi, da rayukan wadanda suka sadaukar da kansu domin baiwa sauran al'umma damar rayuwa, da kuma cimma yanayin zaman lafiya da lumana, da ma ci gaban rayuwar dan Adam baki daya. (Saminu)