Sakatariyar MDD mai lura da harkokin ba da agajin jin kai Valerie Amos, ta ce, MDD na da dangantaka ta kut-da-kut da kasar Sin a fannin ba da agajin jin kai.
Amos wadda ta yi wannan tsokaci yayin zantawarta da manema labaru, gabanin ziyarar da za ta kawo nan kasar ta Sin a karshen watan da muke ciki, ta bayyana fatan samun kyakkyawan darasi daga irin nasarorin da kasar ta samu wajen tinkarar kalubalolin ayyukan jin kai.
Ta ce, kasar Sin na daya daga kasashen dake sahun gaba wajen ba da tallafi ga kasashe ko yankuna masu fama da annoba ko bala'o'i, inda a baya bayan nan ta ba da gagarumar gudummawa wajen yaki da cutar Ebola a kasashen yammacin Afirka dake fama da yaduwar cutar. Irin tallafin da a cewar Amos alfanunsa ba zai misaltu ba. (Saminu)