Wakilin din din din na kasar Sin a MDD Liu Jieyi, ya ce, kasarsa za ta ci gaba da marawa Somalia baya, a yunkurin da ake yi na warware rikicin siyasar kasar, tare da wanzar da dawwamammen yanayin zaman lafiya a sassan kasar.
Mr. Liu ya bayyana hakan ne ga taron manema labarai, jin kadan da kammala zaman kwamitin tsaron MDDr da ya gudana a jiya Laraba, zaman da ya mai da hankali ga tattauna hanyoyin warware matsaloli, da wanzar da ci gaba a Somalia.
Liu ya ce, cikin shekarar da ta gabata Sin ta sake bude ofishin jakadancinta dake birnin Magadishu, fadar gwamnatin Somalia, tana kuma ci gaba da tallafawa kasar da nau'o'in kayayyakin jin kai, da kuma horas da jami'an kasar.
Kaza lika manzon kasar ta Sin ya bayyana irin ci gaban da ake samu, game da aikin wanzar da zaman lafiya a kasar, yana mai jaddada kira ga kasashen duniya, da su ci gaba da tallafawa gwamnatin Somalia, ko a kai ga cimma nasarar da ake fata ta hanyar lumana, a kuma samu ingantar zamantakewar al'ummun kasar. (Saminu)