An saki wadansu yara kimanin 280 da wata kungiya mai dauke da makamai ta kama tana musu horo a kasar Sudan ta Kudu a ranar Talatan nan, in ji asusun yara kanana ta MDD wato UNICEF, yana mai tabbatar da cewa, za a kara sakin wassu nan gaba.
UNICEF wadda ta shiga tsakanin ganin an sako yaran ya yi bayanin cewa, kasho na farko mai dauke da yara 280 da aka saki sun fito ne daga kauyen Gumuruk na jihar Jonglei na kudancin kasar. Sauran rukunin yaran, za'a sake su a cikin wata mai kamawa.
Asusun ya ce, wadannann yaran da kungiyar bangaren adawa na sojin demokradiyar kasar ta kama su da nufin ba su horo suna tsakanin shekaru 11-17. Wadansu sun fara yaki shekaru hudu ke nan, kuma da yawansu ba su shiga makaranta ba.
Yaran sun mika makamansu da kayan su a wani biki da hukumar warware damarar yaki da bangaren adawan na sojin demokradiya da taimakon UNICEF wanda kasar ta Sudan ta Kudu ta kafa. A cikin shekarar da ta gabata, kungiyar tare da wassu kungiyoyi na daba sun debi yara kusan 12,000, galibinsu maza, ana amfani da su a matsayin sojoji.
Fada ya barke a Sudan ta Kudu, kasa mafi kankancin shekaru a duniya a watan Disambar 2013 lokacin da shugaban kasar Salva Kiir Mayardit ya sallami mataimakinsa Riek Machar bisa son mashi laifin juyin mulki .
Fadan da ya yi sanadiyar mutuwar mutane dubu dubata ya kuma raba wadansu miliyan 1.5 daga gidajensu, sannan wadansu fiye da miliyan 5 da matukar bukatan taimakon jin kai.
A ranar 21 ga watan Janairu, bangaren adawa dake mulkin jam'iyyar SPLM ta saka hannu a kan yarjejeniyar samar da zaman lafiya a birnin Arusha dake arewacin kasar Tanzaniya. (Fatimah)