Kakakin rundunar sojin Najeriya Chris Olukolade, ya ce, dakarun sojin kasar sun hallaka wani kusa a kungiyar Boko Haram, bayan wani bata-kashin da sassan biyu suka yi a kusan da garin Alagarno, dake jihar Borno a arewa maso gabashin Najeriya.
Olukolade ya ce, sojojin sun harbe Abu Mojahid da wasu dakarun kungiyar ta Boko Haram, yayin dauki-ba-dadin da ya auku a ranar Talata, lokacin da mayakan suka kai hari kan jami'an tsaron dake sintiri a yankin.
Baya ga mayakan kungiyar da aka hallaka, Olukolade ya ce, an kuma kwace wasu makamai, da ababen hawa da suke amfani da su wajen kaddamar da hare-hare.
A daya hannun kuma kakakin rundunar sojin Najeriyar ya ce, rundunar na ci gaba da kai simame, a sansanoni da maboyar 'ya'yan kungiyar dake wasu dazuzzuka. Ya ce, sakamakon binciken kwakwaf da suke gudanarwa, sojojin na ci gaba da gano wurare da mayakan Boko Haram ke boye makamai.
Ya kuma kara da cewa, ababen fashewa da mayakan ke binnewa a wurare daban daban, ba za su sanya sojoji ja da baya ba, har sai sun kai ga kakkabe yankin na arewa maso gabas daga ayyukan kungiyar baki daya. (Saminu)