in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
An katse kafofin sadarwa na sada zumunta bisa dalilan tsaro a Burundi
2015-04-30 10:24:58 cri

Hukumar dake kula da harkokin sadarwa a Burundi ARCT, ta katse dukkanin kafofin sadarwa na sada zumunta dake kasar, biyowa bayan zanga-zangar kin jinin burin shugaban kasar mai ci na sake tsayawa takara a karo na uku.

A ranar Lahadin da ta gabata ne tarzoma ta barke a kasar, bayan da aka ayyana sunan shugaba Pierre Nkurunziza, a matsayin wanda zai yiwa jam'iyyarsa takara, a babban zaben kasar da ke tafe.

Da yake tabbatar da daukar wannan mataki, babban daraktan hukumar harkokin ta ARCT Deogratias Rurimunzu, ya ce, daga ranar Talata, an dakatar da hanyoyin sadarwar sada zumunta ga 'yan kasar, a wani mataki na inganta tsaro.

Rurimunzu ya ce, tsaro na da muhimmanci maras iyaka, don haka ya zama wajibi a dauki dukkanin matakan da suka wajaba domin tabbatar da shi. Wannan dai dakatarwa ta shafi shafunan zumunta na Whatsapp, da Facebook, da Twitter da kuma Viber.

Ban da wadannan kafofi da masu zanga-zanga ke amfani da su wajen musayar sakwanni, an kuma rufe gidan Radion RPA a ranar Litinin. Kaza lika an rufe kafofin manyan radion FM masu zaman kansu da ke kasar tun daga ranar Lahadi.

Gwamnatin kasar dai ta zargi kafofin da yada bayanai da ka iya rura wutar rikici a kasar.

'Yan adawar kasar ta Burundi dai na zanga-zanga ne domin matsin lamba ga shugaba Nkurunziza, ya yi watsi da aniyarsa ta sake tsayawa takara a karo na uku. (Saminu)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China