Shugaban kasar Burundi Pierre Nkurunziza ya kaddamar da wata makarantar zamani ta fasaha da kwararru wadda kasar Sin ta gina a babban birnin kasar Bujumbura.
Bayan shugaban kasar ya bude makarantar, ya samu damar zagayawa azuzuwan makarantar da aka gina a rukunin gidaje na unguwar Kigobe tare da jakadan kasar Sin a Burundi Yu Xuzhong.
A jawabinsa, jakadan kasar Sin a Burundi Mr. Yu wanda yake bisa hanyar kammala wa'adin aikinsa na jakada a kasar Burundi, ya bayyana gamsuwarsa da kammala ginin makarantar, kuma ya yi alkawarin cewa, kasar Sin za ta baiwa Burundi dalar Amurka dubu 800, domin ta sayi injina da take bukata.
Manyan masu ruwa da tsaki na Burundi sun sami halartar taron, ciki har da ministar kananan makarantu da sakandare Madam Rose Gahiru. (Suwaiba)