Shugaban ofishin kare hakkin bil adama na MDD Zeid Ra'ad Al-Hussein ya yi kira ga daukacin 'yan siyasar kasar Burundi da su kaurace wa tashin hankali gabannin karatowar zaben kasar, ganin yadda dubban 'yan kasar suke tserewa don tsoron sakamakon da zai biyo baya.
Zeid Ra'ad Al-Hussein ya shaida wa taron manema labarai bayan kammala ziyarar aikin shi na kwanaki 4 cewa, yana kira ga daukacin 'yan siyasa da masu fafutukar siyasar kasar na Burundi da su tabbatar da cewar, mahawarar siyasa ba ta kai ga matsayin batanci ga juna da nuna kiyayya ba, balle tashin hankali.
Haka kuma ya bukaci jam'iyyar dake kan karagar mulkin kasar da sauran jam'iyyun adawa, 'yan sanda da sojoji da su tabbatar da matsayin kasar a nan gaba ya zama gaba da komai na bangaren ra'ayin kansu a siyasance. Ya ce, yawan al'ummar kasar ta Burundi sun tsere yanzu haka saboda fargaban rikicin da suke ganin zai iya afkuwa a bayan zaben.
Zeid Ra'ad Al-Hussein ya kuma bukaci jami'an tsaron kasar da su hana ayyukan bangaren matasa na jam'iyya mai mulki da ake kira Imbonerakure, in har ana son yin zaben cikin kwanciyar hankali, yana mai jaddada cewar, dole ne gwamnatin Burundi ta isar da sako a bayyane ga wannan kungiyar mai hadarin gaske na cewar, ba za ta amince da ayyukanta ba da kuma fiffikon da take dorawa a kan wassu ayyukanta.
Burundi dai za ta aiwatar da babban zabenta tsakanin ranakun 26 na watan Mayu da 24 na watan Agusta, sannan za'a yi na shugaban kasa a ranar 26 ga watan Yuni. (Fatimah)